29 Maris 2021 - 19:53
Yarjejeniyar Da Aka Kulla Tsakanin Iran Da China Ta Fi Mayar Da Hankali Wajen Samar Da Daidaito Na Karfi A Siyasar Waje

Kakakin majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Baqer Qalibaf, ya bayyana cewa; Yarjejeniya mai muhimmanci da aka kulla a tsakanin Iran da kasar China tana a karkashin siyasar Iran ta waje ne ta kulla alaka mai karfi da kasashen gabashin duniya da na yankin Eurasia domin samun daidaito na karfi a fagen siyasar duniya.

ABNA24 : Kakakin majalisar ya kuma jaddada muhimmanci yin aiki tukuru domin aiwatar da dukkanin bangarorin yarjejeniyar ta hanyar aiki a tsakanin kasashen biyu.

A jiya Asabar ne dai ministan harkokin wajen kasar China Xi Jinping da ya kawo ziyara Iran, da kuma Muhammad Jawad Zarif su ka rattaba hannu akan yarjejeniyar aiki tare da Iran, ta tsawon shekaru 25.

Bangarorin da yarjejeniyar ta shafa sun kunshi al’adu, sharia’. Tsaro, soja da kuma aiki a fagagen yanki da kuma siyasar kasa da kasa.

342/